(ABNA24.com) Ma’aikatar harkokin wajen kasar Turkiya ta bayyana haka ne a matsayin mayar da martani dangane da nada kansa shugaban sojan kasar Libya da janar Halifa Haftar ya yi, bayan da ya ce ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ta Sukhairat.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Turkiya ta kara da kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su gaggauta daukar mataki akan Haftar da hana shi kafa tsarin kama-karya na soja a kasar Libya.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai janar Halifa Haftar ya shelanta yin watsi da yarjejeniyar Shukhairat wacce aka kulla a tsakanin dukkanin bnagarorin da su ke rikici da juna na kasar Libya a 2005 a can kasar Moroko.
Har ila yau Janar Halifa Haftar ya bayyana cewa ya amince da wakilcin da al’ummar kasar su ka ba shi na ya zama babban kwamandan sojan kasar, sannan kuma shugabanta.
/129
Turkiya : Kwadayin Mulkin Kama-Karya Na Soja Ne Ya Sa Halifa Haftar Yin Watsi Da Yarjejeniyar Sukhairat
2 Mayu 2020 - 03:52
Lambar labari: 1032229
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Turkiya ta bayyana haka ne a matsayin mayar da martani dangane da nada kansa shugaban sojan kasar Libya da janar Halifa Haftar ya yi, bayan da ya ce ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ta Sukhairat.